Majalisar Dokokin Jihar Kano Ta Canza Wa Jami'ar KUST WUDIL Suna

Publish date: 2024-05-17

Kano - Majalisar dokokin jihar Kano ta amince da canza sunan Kano University of Science and Technology, Wudil (KUST) zuwa sunan fitaccen ɗan kasuwan nan, Aliko Ɗangote.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa hakan ya biyo bayan wasikar da bangaren zartarwa ya aike wa majalisar domin neman sahalewar zauren na canza sunan jami'ar zuwa Aliko Dangote University of Science and Technology, Wudil.

Mambobi sun tattauna kan batun kana suka zartas da canza sunan makarantar yayin zamansu bisa jagorancin shugaban majalisar, Honorabul Hamisu Chidari.

Kara karanta wannan

Tsautsayi: Wani Matashi Ya Naushi Abokinsa, Ya Faɗi Ya Mutu a Birnin Kano

Da yake hira da manema labarai jim kaɗan bayan fitowa daga zauren, shugaban masu rinjaye, Labaran Madari, yace shi da takwarorinsa sun amince da kudirin gwamnatin jiha na canza sunan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma yi bayanin cewa yan majalisun sun amince da bukatar gwamnatin jihar ne bayan la'akari da ɗumbin gudummuwar da Ɗangote ke bayar wa a ɓangaren ilimi.

Tun yaushe gwamnatin Kano ta so canza sunan KUST?

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa tun a watan Mayu, 2022, kwamishinan yaɗa labarai na jahar Kano, Muhammad Garba, ya sanar da kudirin gwamnati na canza sunan makarantar.

Yace sun yanke haka ne bayan kwamitin da ya ziyarci jami'ar ya gabatar da shawarwarinsa ga mai girma gwamna, Dakta Abdullahi Ganduje.

Haka zalika ya bayyana cewa tuni ɓangaren zartaswa ya aike da shirin canza sunan ga majalisa domin ɓangaren masu doka su gudanar da aikinsu kamar yadda doka ta tanada.

Kara karanta wannan

Ta Fasu: Kalaman da Tinubu Ya Nemi Tawagar Matan APC Su Faɗa Wa 'Yan Najeriya Masu Neman Canji a 2023

Jami'ar KUST Wudil

A shekarar 2001, gwamnatin jihar Kano ta kafa jami'ar da sunan, Kano University of Technology, amma a 2005 aka canza mata suna zuwa Kano University of Science and Technology Wudil.

A 2008, Tsohon gwamna, Ibrahim Shekara, ya naɗa Dangote a matsayin shugaban jami'ar (Chancellor) kuma gwamnan yanzu, Abdullahi Ganduje, ya sabunta naɗin a watan Nuwamba, 2021.

A wani labarin kuma Lauyan ƙungiyar Malaman Jami'o'i ta ƙasa yace nan ɗa yan kwanaki za'a kawo ƙarshen yajin aikin ASUU

Babban lauya Femi Falana ya bayyana kwarin gwiwar cewa, nan ba da dadewa kungiyar malaman jami'a karkashin ASUU za su janye yajin aikin da suke yi tun watan Fabrairun bana.

Falana ya bayyana cewa, janye yajin aikin ba wai makwanni zai dauka ba, zai zo ne cikin 'yan kwanaki masu zuwa nan kusa.

Asali: Legit.ng

ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC6xLCqaGlkboR0go9mpJqikaG2tK3RZpuoo5%2Bgtq95yaKfmqpdoK6vu4ytmGabkaPHonnWmmSjmZ2errN5yq6qrWWnqrGquIysrKeZXw%3D%3D