Wike Ya Amince Da Nadin Barr. Benedict Dauda a Matsayin Mataimaki Na Musamman

Publish date: 2024-08-31

FCT, AbujaNyesom Wike, ministan babban birnin tarayya Abuja, ya amince da naɗin Barr. Benedict Daudu a matsayin babban mataimaki na musamman kan harkokin shari'a da hadin gwiwa tsakanin ɓangarori da dama.

Hukumar ta FCTA ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta sanya a shafinta na X (wanda a baya aka fi sani da Twitter) a ranar Talata, 10 ga watan Oktoba, inda ta ƙara da cewa naɗin ya yi daidai da amincewa da ƙwarewar Daudu da tsohon gwamnan jihar Rivers na wa'adi biyu ya yi.

Kara karanta wannan

Malamin Makaranta Ya Ɗebo Ruwan Dafa Kansa Bayan Ya Zane Ɗaliba Mace a Abuja

Me yasa Wike ya naɗa Daudu wannan muƙamin?

Daudu ya kasance yana da ƙwarewa sosai ta fannin ilmi kuma masani ne kan manufofi masu muhimmanci da suka shafi ƙasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar ta FCT ta bayyana lauyan da cewa:

"Barr. Benedict Daudu, fitaccen lauya wanda ke aikinsa na lauya a Najeriya, zai kawo kwarewa sosai da ilmi a sabon aikinsa."

Nadin Wike a matsayin minista a gwamnatin shugaba Bola Tinubu dai ya jawo an yi ta tafka cece-kuce, saboda kasancewarsa jigo a jam'iyyar adawa ta PDP.

Sanatan Abuja ta caccaki Wike kan naɗe-naɗe

Sanata Ireti Kingibe mai wakiltar birnin tarayya Abuja, ta aike da sabon gargaɗi ga Nyesom Wike kan naɗe-naɗen sakatarorin hukumar FCTA da ya y.

Sanatan ta gargaɗi Wime kan wuce gona da iri inda ta nuna masa cewa yana buƙatar amincewar majalisa kafin ya yi hakan.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba Gida-Gida Ya Sanar da Ranar Ɗaura Auren 'Yan Mata da Zawarawa 1,800 a Kano

Wike Ya Caccaki Ma'aikata

A wani labarin kuma, ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Ezenwo Wike, ya caccaki ma'aikatan da ke zanga-zanga kan sauke shugabannin wasu hukumomi da ya yi.

Ministan ya bayyana cewa babu wani tausayi ko tunani wanda zai hana shi aikata abin da shi ne daidai.

Asali: Legit.ng

ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC6xLCqaGllaoR6hJdmrqKjlWLGonnApqCnm5VisaJ5zZqboqZdl66zvoybnKedlJ6wtXnDmqydmV2Weq6t06yYsqGeYrqiwMCipJqjmWK7onnMrqqapZ2Wu3A%3D